Kamar Yadda Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA-ya habarta cewa, dubban ‘yan kasar Pakistan da suka fusata sun kona ofishin ‘yan sanda bayan da wani mutum ya wulakanta kur’ani. Akalla mutane 5,000 daga Khyber Pakhtunkhwa ne suka taru a wajen ofishin ‘yan sanda domin neman a mika mutumin da ya wulakanta kur’ani, amma ‘yan sanda sun yi watsi da bukatar. Daga nan ne masu zanga-zangar suka kona ofishin ‘yan sanda tare da kona motoci da dama.

1 Disamba 2021 - 14:17